Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Akalla 14 A Damaturu.

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

15 people like this topic, 19 people dislike this topic

3direct
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 4:34 pm

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Akalla 14 A Damaturu.

Postby 3direct » Mon Jul 27, 2015 1:03 pm


Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Akalla 14 A Damaturu.Al'amarin ya auku ne a kofar shiga kasuwar lokacinda ake kokarin tantance yarinyar.

'Yan kato da gora suka kafa shingaye a Maidguri.

'Yan kato da gora suka kafa shingaye a Maidguri.

Aliyu Imam


Wasu nakiyoyi da wata 'yar  kunar  bakin wake ta tayar a wata kasuwa a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, sun kashe akalla mutane 14.

Shaidun gani da ido suka ce akalla mutane 50 ne suka jikkata.

Jami'ai a jihar suka ce fashewar  ta auku ne da safiyar  lahadin nan a kofa shigar  kasuwar dake Damaturu babban binrin jihar Yobe.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin. A farkon wannan wata akalla mutane 9 ne suka halaka lokacinda  wata 'yar  harin kunar  bakin wake ta auna masu masu sallar idi.

Ga karin bayani.
harin bam a Damaturu

 

Ahalinda ake ciki kuma wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a harabar  wani O'tel a Mugadishu a ranar lahadin nan, ya kashe akalla mutane 13.

A cikin O'tel din ne kuma ofisoshin jakadancin kasashen China da Masar  suke.
Kungiyar  mayakan sakai ta al-shabab ta dauki alhakin kai wannan hari.

 

 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 1 guest

cron