An Bude Taron Matasa Da Majalisar Dinkin Duniya Take Goyon Baya A Abuja.

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

12 people like this topic, 26 people dislike this topic

3direct
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 4:34 pm

An Bude Taron Matasa Da Majalisar Dinkin Duniya Take Goyon Baya A Abuja.

Postby 3direct » Mon Jul 27, 2015 1:05 pm


An Bude Taron Matasa Da Majalisar Dinkin Duniya Take Goyon Baya A Abuja.Shugaban taron na kasa Hon Charles Folayo yace an shirya taron ne domin duba muradun kasa.

Wasu matasa 'yan gwagwarmaya suke zanga zanga a Abuja.

Wasu matasa 'yan gwagwarmaya suke zanga zanga a Abuja.

Aliyu Imam


Da yake magana kan dalilin shirya taron shugaban taron kasa, Hon Charles Olufemi Folayo, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina cewa, burin taron shine tattaunawa kan makomar  matasa a Najeriya

Mr. Folayo yace sanin cewa matasa sune kashin bayan kowace al'uma, ya zama tilas a maida hankali kan muradunsu domin sune zasu kawo ci gaban tattalin arziki da habaka hanyoyin kawo ci gaban al'uma da kasa.

Wasu daga cikin masu halartar taron sun bayyana cewa suna halarci taron domin su tattauna kan bukatunsu. Kamar yadda wakiliya a majalisar  matasan, Fatima Maina Abdullahi tayi bayani. Ta bayyana fatar  zuwa karshen taron zasu fito da matsaya dangane bukatun matasa.

Wata wakiliya daga jihar Edo tace ta halarci taron ne da zummar karuwa kan muhimman bukatun matasa.

Ga karin bayani.
Taron matasa na kasa

 

 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 2 guests

cron