Gaskiya Ne, Ina So In Raba NNPC – Buhari

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

24 people like this topic, 32 people dislike this topic

tola
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 11:41 am

Gaskiya Ne, Ina So In Raba NNPC – Buhari

Postby tola » Mon Jul 27, 2015 2:43 pm

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amsa jita-jitar cewa zai raba Kamfanin Mai na kasa (NNPC).

Shugaba Buhari ya bayani karancin mai a matsayin daya daga cikin abunda gwamnatin shi zata magance. Cewar shugaban: “Najeriya nada matatu guda 4, mafi yawan su an sace abubuwanda ke ciki. Hakan ke sanya yan kasuwa su je su sawo Man a kasuwar bayan fage.”

Shugaba Buhari ya bayana akan ne a wata hira da akayi dashi a yau a ”NTA morning show.” Ya bayyana cewa, ta’addacin tsagerun Niger delta na hana Nigeria cin matukar amfanin albarkatun Mai. Da aka tambaye shi mi yake so ya gani cikin wadanda zai ba Ministoci, sai yace: “Muna son masu kwazo, wadan suka san makamar aiki, masu sadaukar da Kansu. Da yawa daga cikin ma’aikatun gwamnati an latata su. Kowa kanshi ya sani. Wasu suna neman su zama ubangiji akan mu. Abun takaici ne cewa mutanen kirki ne, masu gwarzo da sadaukarwa, amma kowa aikin gaban shi kawai yakeyi. Dole ne mu duba gogaggun ma’aikata, yan siyasa da mutanen kirki  domin su jagoranci ma’aikatun gwamnati da sauran sasan gwamnati. Zamuyi iya bakin kokarinmu wajen nada mutane wadanda suka taba aiki cikin gwamnati. Abun takaici ne mutane da yawa da yakamat ace an nada su ba’a nada su ba. Amma yanzu zamuyi kokari wajen rage hakan.”

Da aka tambaye shi akan rikicin majalisar kasa sai yace: “Mu zamu bi kundin tsarin mulkin kasa yadda ya kamata. Sanan kuma yayi kira ga Saraki da Dogara akan suyi biyyaya ga Jam’iyya su kauda burin Kansu subi na Jam’iyya. Hanyar kawai da zani iya sanya baki acikin harkar majalisa shine inyi kira garesu akan wannan abunda ke faruwa. Bai kamata mu (APC) muyi kasa a gwiwa ba. Baza mu fadi wannan fadan ba. Baza mu kyale PDP ta anshe gwamnati ba saboda ana rikici ba. Baza mu bari burinmu na kanmu ya lalata nasarar da muka samu ba.”

Da aka tambayeshi game da kalubalan daya fuskanta wata biyu da hawanshi, sai yace: “Daman abunda muka gani shine muke tsammani. Rashin tsaro, rishin aikin yin matasa, da kuma rashin kudi aljihun gwamnati.” 

A wani labarin kuma shugaba Buhari ya zargi wasu tsofaffin Ministoci da saida haramtaccen mai har Durom miliyan Daya a kowace rana. Kudin da aka samu kuma su sanya cikin Akawunt dinsu. Shugaban kuma ya dauki alwashin gurfanar da wadanda aka kama a gaban kuliya.

Buhari ya zargi cewa: “Sama da Durum 250,000 na mai ake sacewa ana saidawa sannan kudin kuma a Sanya a cikin aljihunsu. Sannan kuma yace  Amurka da sauran kasashen da suka cigaba suna taimakama Najeriya wajen gane Akawunt din.”

background

T


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 3 guests

cron