Mataimakin Gwamnan Borno Ya Rasu

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

26 people like this topic, 38 people dislike this topic

3direct
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 4:34 pm

Mataimakin Gwamnan Borno Ya Rasu

Postby 3direct » Sat Aug 15, 2015 9:09 pm


Mataimakin Gwamnan Borno Ya RasuGwamnatin Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha.

FILE

FILE
Marigayin ya rasu a birnin Yola dake Jihar Adamawa, a lokacin da yake ziyarar aikina bikin yaye dalibai da aka yi Asabar dinnan.Bayan kwanciya da dare a makwancinsa, wayewar gari ke da wuya aka bincika aka ga ya rasu.

An yi korin neman Alhaji Zanna ta waya, bai dauki waya ba, kuma babu alamunsa ko motsin sa. Bayanan da muka samu sun bayyana mana cewa an karya kofar dakin da yake ciki, a nan ne aka same shi babu rai.

Ya zuwa yanzu babu bayanai dangane da ko yana fama da wata rashin lafiya. Saboda ko shekaran jiya a birnin Maiduguri, an yi zagayen aiki da shi a wasu kauyuka tare da gwamnan Jihar.

Marigayin yayi ayyuka da dama kafin ya tafi garin Yola. Bayanai da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya samu na cewa babu wani rashin lafiya da yake tattare da shi, wanda ake zaton shi ne yayi sanadiyar rasuwar sa.
Mataimakin Gwamnan Borno Ya Rasu – 2’30”

 

 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 2 guests

cron