Buhari Ya Bayyana Yiyuwar Gano Yan Matan Chibok Da Wuri

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

16 people like this topic, 36 people dislike this topic

3direct
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 4:34 pm

Buhari Ya Bayyana Yiyuwar Gano Yan Matan Chibok Da Wuri

Postby 3direct » Wed Aug 19, 2015 2:48 pm

Wadanda suke shirya zama domin tuna Yan matan Chibok da Yan Boko Haram suka sace sun bayyana cewa suna da tsammani mai kyau akan gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

details

Manyan mashiryantan sun bayya yiyuwar dowowar Yan matan nan bada jimawa ba saboda kokarin da shugaban kasan yake yi.

Sun bayyana hakanne a Abuja a wata takar wadda suka fidda mai dauke da sa hannun Oby Ezekwesili da kuma Hadiza Bala Usman. Un kuma bayyana cewa shirya bikin cika kwana 500 na Yan mata a hannun waanda suka sace su:

“Domin bikin cika kwana 500 na Yan matan,zamu shirya sallar La’asar a ranar Juma’a, da kuma adduar coci a Unity fountain domin gudanar da  addu’o’i. Sannan kuma zamu shuka Itace tare Sakataren Majalisar dinkin duniya da dai sauransu.”

Masu shirya abun kuma sun bayya cewa cika bikin kwana 500 anyi mashi take da, kwana 500 Har yanzu dai, ana kokarin ceton ku, baza a taba manta kuba, a maido mana da Yan matan mu, (“500 Days On, Chibok Girls — Crying To Be Rescued, Never To Be Forgotten.”)

Sun shawarci kowa yayi kokarin da zaya iya domin a dawo da yan matan. Sannan suka bayyana cewa Jajayen riguna za’a sanya a ranar.

Sun kuma bukaci masu aikin da kafafen sada zumunta suyi amfani da taken bikin domin su taimaka da fadakarwa.

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

background

 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 1 guest

cron