Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Talata 18 Ga Watan Agusta

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

23 people like this topic, 30 people dislike this topic

tola
Posts: 0
Joined: Thu Oct 30, 2014 11:41 am

Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Talata 18 Ga Watan Agusta

Postby tola » Wed Aug 19, 2015 2:49 pm

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata 18 ga watan Agusta. Ku duba domin ku same su.

 

1. Wata tsohuwa da dawa da ranta lokacin binne ta.

wata tsohuwa mai suna Gogo Tshuma wadda ke a kauyen  Chikamba a Jambezi, Kasar Zimbabwe ta dawo da ranta lokacin da ake bikin binne ta.

2. Wata babbar Yar APC ta bayyana damuwar ta akan rayuwar Buhari.

Naja’atu Muhammad, wata jiguwar Yar APC dake Kan ta bayyana kokarin da wasu sukeyi domin su ruguza kokarin da shugaban kasa Buhari yakeyi domin ya yaki rashwa.

3. David Mark ya bayyana a Kotu.

Tsohon shugaban Majsalisar Dattawa David Mark ya bayyana a gaban Kotun zabe dake Benue domin kare cin zaben shi na 5.

4. Abunda Yan Boko Haram suka fada mani -Barista A’isha.

Barista A’isha Wakil wadda ke aiki da kwamishan din kare hakkin bil Adama ta bayyana yadda rayuwar wasu Yan Boko Haram take kafin su shiga kungiyar.

5. Babu wanda ya rayu a hatsarin Jirgin sama a Indonesia.

Jami’an cdeto na gaggawa na Indonesia sun bayyana cewa sun gano gawar mutane 54 a wani sashen jirgin daya fadi a Papua, Indonesia.

6. Bidiyon Kai Hare-hare a Sambisa.

Jami’an sojin sama sun saki wasu Bidiyoyi dake nuna sojojin suna kai ma dajin Sambisa hare-hare a cikin jirgin sama.

7. Matar Fasto ta kama shi yana fasikanci.

Matar wani Fasto mai suna Doris Oseni ta kama mijinta Fasto Femi Oseni yana fasikanci da wata mata a cikin Coci, Ta nemi Kotu data raba masu aure.

8. Wani Yaro ya rubuta ma Yan Boko Haram wasikamai ban tausai.

Wani Yaro mai suna Sope dan shekara 9 ya rubuta wata wasika mai ban tausai ga Yan Kungiyar Boko Haram.

9. Mutane 150 sun rasu, wasu sun jikkata a lokacin da suke kokarin ruga ma Yan Boko Haram.

sama da Mutane 150 ne suka mutu a lokacin da suke kokarin kaucema Yan boko Haram a lokacin da suka kai ma kauyansu hari wanda yake cikin Jihar Yobe.

10. Abunda Buhari ya fada mani – Abdulahi Dikko Inde.

Tsohon shugaban Kastam Abdullahi Inde ya bayyana abunda shugaba Buhari ya fada mashi a lokacin da ya kai masa takardar barin aiki.

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 1 guest

cron