Page 1 of 1

Ana Zaben Sarki Oni na Ife

Posted: Sat Aug 22, 2015 11:31 pm
by adefisayo

Ana Zaben Sarki Oni na IfeHukumomi a Jihar Osun da masarautar Ife suna ci gaba da aikin zabe da nada sabon sarki bayan rusuwar Oni na Ife Oba Sijuwade.

FILE

FILE
Ana haka ne kuma wata tawagar wakilan Majalisar Dittijai ta je jihar domin mika ta’aziyyar mutuwar basaraken.Sanata Abdullahi Adamu ne ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar, yace “duk wanda ya san marigayin, ya san cewa yana da mutunci, daraja, gaskiya da rawar da ya taka wajen hada kan Najeriya. Mutum ne baya harshen damo.”

Shi kuwa Sakataren gwamnatin Jihar Osun Alhaji Mashood Adeyoti da yayi wa Sanatocin maraba lale ya bukaci shuwagabannin da su ajje ban-bance ban-bancensu a gefe su yiwa kasar aiki don a sami cigaba.

Shugaban majalisar dokokin Jihar Osun Najim Salam yace wannan ziyarar ta’aziyyar ta nuna hadin kan Najeriya.

“Hadin kan Hausawa da Yarabawa zai karfafa hadin kan kasar nan, kuma wannan zai nuna ma duniya cewa kan mu a hade yake” a cewar Mr. Salam.
Ana Zaben Sarki Oni na Ife – 2’15”