Rashawa ce ta haddasa kungiyar Boko Haram – Soyinka

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

22 people like this topic, 36 people dislike this topic

User avatar
wikinaira
Posts: 2454
Joined: Mon Sep 10, 2012 3:44 pm

Rashawa ce ta haddasa kungiyar Boko Haram – Soyinka

Postby wikinaira » Thu May 26, 2016 2:09 pm

Image
Farfesa Wole Soyinka

Farfesa Wale Soyinka ya bayyana cewa rashawa ce ta haddasa kungiyar Boko Haram saboda akwai gibi tsakanin shugabanin da kuma wadanda ake shugabanta. jaridar Pulse.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari bata da wani tsarin tattalin arziki

Ya bayyana hakan ne a Oslo, babban birnin kasar Norway inda ake gudanar da wani taro mai take “The road to Justice”, “Hanyar samun adalci” inda soyin ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta tsiro ne sakamakon ” Rashawar dake aukuwa da yawa a cikin gwamnatin.

Wale Soyinka ya samu gaisuwa daga jama’a daga masu yawa inda yayi masu bayanin ma’anar Boko Haram inda ya bayyana cewa Boko ana nufin ilimin zamani. Ya bayyana cewa yan kungiyar suna fada ne da ilimin zamani inda suke kokarin hana mutane samun wannan ilimin.

Ya kuma bayana cewa gibin dake tsakanin shugabannin da al’ummar su ne ya hadda sa hakan.

rahoto ya nuna cewa sama da mutane Dubu 13 ne yan kungiyar Boko Haram suka kashe a cikin shekaru 7 da sukayi suna aikata kisa akan al’ummar yankin kudu maso Gabashin Najeriya. Sannan kuma suka bayyana cewa yan kungiyar sakamakon rikici da suke haddasawa sun kori sama da mutane Miliyan 3.5 daga gidajen su.

Amma sojojin Najeriya na cin nasara akan yan kungiyar domin a yanzu ta shiga har dajin Sambisa inda suka ruguza matsugunnin yan kungiyar inda suka kashe wasu kwamandojin kungiyar wadansu kuma aka kama su.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya da Gwamnonin jihohin Arewa Maso Gabshin Najeriya, musamman Borno, Yobe da Adamawa. Gwamnatocin sun bayyana cewa zasu ware duka kudaden da ake nema don tabbatar da taimaka ma mutanen wurin


I don't try to make my presence to be noticed, I only strive to make my absence to be felt http://www.wikinaira.com

Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 1 guest

cron